Menu
Gwamna mai barin gado na jihar Osun, AbdulRauf Aregesola ya bayyana cewa bai taba karbar albashi ba tun lokacin da ya hau kujerar gwamna kuma ya kwashe shekaru takwas yana mulkin.
“Jihar ke ciyar da ni, ta saka min man fetur a mota ta kuma samar min da muhalli. Idan an dauke min dukkan wadannan, bana bukatar kudi.

“Ba ni da asusun ajiyar banki a ko ina. Ba ni da gida illa wanda na gina kafin na zama gwamna. Duk mai so yana iya zuwa ya yi bincike idan ina da asusun ajiya a banki.” inji Aregbesola.
Ko Sauran Gwamnonin Nijeriya Haka Suke?
#Rariya

Post a Comment

 
Top