Menu
A jiya Alhamis ne 29/11/2018 Rundunar ‘an sandan jihar Kano ta sami labarin wani gida a Unguwar Ladanai, Hotoro, inda wani Inyamuri ya kama hayar wani gida yana kawo kaya cikin dare sannan wasu mutane na kawo masa ziyara.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, SP Magaji Musa Majia yace rundunar ta karbo takardar izinin bincike daga kotu, inda suka balle gidan kuma aka sami tabar wiwi buhu 25 mai dauke da kunshi 25 kowanne, jimilla kunshi 625 kuma kimar kudinta ya kai naira miliyan takwas.

Rundunar ta kuma ja hankalin jama’a da su ci gaba da sa ido da kuma taimakawa ‘yan sanda don shawo kan matsalolin tsaro a kowanne lungu da sako kamar yadda Mai Martaba Sarkin Kano ya yi yi umarni.
Daga karshe rundunar ta jinjinawa al’ummar Ladanai, Mai Unguwar Ladanai da Dagacin Hotoron Arewa bisa gagarumar gudunmawar da suka bayar wajen gano wannan gida da ake boye kayan laifi.
#Rariya

Post a Comment

 
Top